SHARE

A safiyar ranar Talata ne aka samu gobara a kasuwar Bayan Tasha da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Gobarar ta tashi ne bayan an kawo wutar lantarki da misalin karfe 2:00 a.m, inda ta lashe shaguna akalla guda 50.

Wasu da al’amarin ya faru a kan idanunsu, sun tabbatar da cewa yan kasuwa sun tashi, kuma an rufe shaguna a lokacin da gobarar ta faru.

Hukumar kashe gobara ta yi nasarar kashe wutar, wanda hakan ya kare karuwar asara ko rasa rayuka a yayin gobarar.

Ita ma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jiha (SEMA), ta fara daukar bayanan irin asarar da aka samu yayin gobarar da kidaya shagunan da su ka kone.

Gobarar Bayan Tasha ya faru ne bayan shekara daya da samun wata gobara a kasuwar, tare da jawo asara mai tarin yawa.

Gobara ta lashe shaguna 50 a jihar Yobe

NO COMMENTS