SHARE

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya jaddada aniyar gwamnatin tarayya na farfado da ilimin kimiyyar kere-kere ta hanyar samar da cikakkun kayan aiki ga dukkanin kwalejojin kimiya mallakin gwamnatin tarayya.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a lokacin da yake kaddamar da dakin karatu mai hawa daya da dakin gwaje-gwaje da kuma siyan kayan aikin da dakin gwaje-gwajen zai bukata a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya dake Bali, a jihar Taraba.

Alausa wanda Daraktan Ilimin Kimiyya da Fasaha Dr.Ejeh Usman ya wakilta ya ce gwamnati ta kashe zunzurutun kudi har Naira miliyan 390 domin gudanar da aiyukan.

Ya ce gine-gine da kayan aikin da aka samar za su inganta ayyukan koyo da bincike a cikin kwalejin.

Ministan ya bayyana cewa, Federal Polytechnic Bali ce ta biyu wajen cin gajiyar asusun farfado da aikin kwalejojin wato NEEDS domin bayan polytechnic ta Kaduna.

Alausa ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta jajirce wajen baiwa ilimi fifiko wanda shine ginshikin ci gaban kasar.

Alausa ya ci gaba da cewa, “Ina kira ga mahukuntan wannan kwaleji da ku yi amfani da wadannan wurare don koyar da daliban ku yadda ya kamata tare da tabbatar da dorewar kayan”

Gwamnatin Tarayya ta dauki aniyar inganta ilimin kwalejojin kimiya da fasaha

NO COMMENTS