SHARE

Karamin Ministan Ayyuka, Mohammed Bello Goronyo, ya yi gargadi ga ‘yan kwangilar da ke tafiyar da ayyukan Hukumar Kula da Titina ta Tarayya (FERMA) da su cika alkawuran da suka dauka ko kuma su fuskanci sakamakon.

Goronyo ya bayyana hakan yayi ziyarar aikin da ya kaiwa ofisoshin hukumar a shiyyar kudu ya yamma ya kuma jaddada cewa zamanin watsi da ayyukan kwangila yazo karshe.

Ya tunatar da ’yan kwangilar cewa kudaden da za a gudanar da wadannan ayyuka suna fitowa ne daga masu biyan haraji, wadanda suka cancanci su girbi cikakkiyar darajar kudadensu.

Ministan ya umurci FERMA da ta gabatar da cikakken jerin sunayen ‘yan kwangilar da suka kasa karasa ayyukansu ga ofishinsa cikin mako guda domin daukar matakin da ya dace.

Ya kuma yi kira da a kafa kwamiti na musamman don sa ido kan kwangilolin hanya a duk fadin kasar, tare da tabbatar da ingancisu da kammala su akan lokaci.

Goronyo ya yi alkawarin gudanar da ziyarar da zata a wuraren da ake gudanar da ayyukan domin tantance ayyukan ‘yan kwangilar da kansa. Ya kuma bai wa ma’aikatan FERMA tabbacin cewa walwalarsu tana sa muhimmanci ga ma’aikatan ayyukan saboda haka zai dauki matakan kawo karshen dukkan kalubalen da suke fuskanta.

Gwamnatin Tarayya ta gargadi Yan kwangilar dake aiki da FERMA su tabbatar sun kammala ayyukansu

NO COMMENTS