Gwamnatin jihar Zamfara da kungiyar kwadago (NLC) sun sanya hannu a kan yarjejeniyar mafi karancin albashin N70,000.
Gwamnatin karkashin gwamna Dauda Lawal ta ce sai a watan Maris, 2025 za ta fara biyan mafi karancin albashin, bayan an kammala tantance ma’aikata.
A nata bangaren, kungiyar NLC reshen jihar Zamfara ta umarci ma’aikata da su jingine shiga yajin aikin da kungiyar ta kasa ta ba su umarni.
Zamfara ta na daga cikin jihohin Najeriya 12 da kungiyar NLC ta kasa ta bayyana cewa za a gudanar da yajin aiki, saboda kin biyan ma’aikata mafi karancin albashi.
Gwamnatin Zamfara za ta fara biyan mafi karancin albashi a 2025 – NLC