SHARE

Ma’aikatan NPOWER karkshin gwamnatin tarayya sun dakatar da shirin tsunduma yajin aiki har zuwa karshen watan Janairu.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar ya fitar a litinin din nan, inda yace sun zauna da wakilan gwamnatin tarayya kuma an samu matsaya kan batun biyan hakkokin ma’aikatan da ya makale.

Da yake yiwa DAILY POST HAUSA karin bayani a yammacin jiya, shugaban kungiyar na jihar Kano Kwamared Jibrin Ali Jibrin yace sun zauna da wakilan gwamnati da suka hada da sanatoci da yan majalisu da ministan
Jinkai kuma sun yanke shawara dakatar da zanga zangar,

Yace gwamanti zata biya bashin kudaden da suke binta a watan Janairu, wannan dai ya kawo karahen barazanar da ma’aikatan suka yi tun da fari, sai dai Jibrin Ali Jibrin yace zasu koma kan bakansu idan gwamanti ta saba alkawarinta

Ma’aikatan N-POWER sun dakatar da shirin tsunduma yajin aiki – Kwamared Jibrin A. Jibrin

NO COMMENTS