SHARE

Hafsat Bello Muhammad

Ƙungiyar kwadago ta kasa NLC ta bayyana shekarar 2024 a matsayin mafi sarkakiya a rayuwar ma’aikatan.

Shugaban ƙungiyar Joe Ajaero ne ya bayyana hakan a wani taron yan kwadago da aka gudanar a Abuja a ranar litinin.

Yace yan kwadago a fadin kasarnan sun sha matukar wahala a 2024, irin wadda basu taba gani ba.

“A wannan shekarar mun hadu da tasku iri-iri. An tuhume mu, an bincike mu, an ci zarafin mu kuma anyi kokarin firgita mu” a cewar Ajaero.

A wannan shekarar ne dai yan kwadagon sukayi fafutukar ganin an kara sabon mafi karancin albashi zuwa dubu saba’in ga dukkan ma’aikata a kasar nan.

Shekarar 2024 ce mafi muni ga ‘yan Kwadago’ – Joe Ajaero

NO COMMENTS