Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya sanar da wani sabon tsari na biza ga ‘yan Najeriya, inda ya ce masu zuba jari da masu yawon shakatawa za su iya neman biza ba tare da sun gabatar da fasfo dinsu ba.
Wannan sabon tsarin an tsara shi domin saukaka harkokin tafiye-tafiye da kuma karfafa hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Ramaphosa, ya bayyana wannan sabon tsarin ne a ranar Talata, yayin bude zaman taro na 11 na Kwamitin Hadin Gwiwa tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu (BNC) a birnin Cape Town.
Wannan taro ya hada shugabannin biyu da sauran manyan jami’an gwamnati daga kasashen biyu don tattaunawa kan muhimman batutuwan da suka shafi cigaban kasashen.
Taron ya samu halartar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya yi karin haske kan muhimmancin kyautata alakar diflomasiyya da tattalin arziki tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu.
Shugaba ya jaddada cewa wannan sabon tsarin zai taimaka wajen bunkasa zuba jari da bunkasar kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.
Bugu da kari, wannan sabon tsarin biza na daga cikin matakan da gwamnatin Afirka ta Kudu ke dauka domin kara bude kofar shiga kasar ga masu neman damar kasuwanci da yawon bude ido. Hakan zai kuma taimaka wajen rage cikas ga ‘yan Najeriya da ke sha’awar ziyartar kasar domin dalilai daban-daban na cigaba.
Wannan bayani ya fito ne daga mai taimakawa ahugaban kasa kan yada la arai Bayo Onanuga wanda ya Rawaito Shugaba Tinubu na bayyana cewa gwamnatin Najeriya na maraba da wannan cigaba, tana mai fatan cewa hakan zai kara dankon zumunci da kuma inganta alakar kasuwanci da zamantakewa tsakanin kasashen biyu.
Afirka ta Kudu ta saukaka bada bisa ga yan Najeriya