SHARE

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yabawa kyakkyawan nasarar ilmantarwa da ɗaliban da gwamnati ta dauki nauyin su don ci gaba da karatu a Indiya.

A ziyarar da ya kai wa daliban a jami’ar Sharjah da ke kasar Indiya, Gwamnan ya nuna matukar alfahari da sadaukarwar da suka yi da kuma nasarorin da suka samu, inda ya bayyana nasarar da suka samu a matsayin hujja karara na fa’idar saka hannun jari a fannin ilimi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Nature ya fitar a ranar Laraba, Yusuf ya tabbatar da cewa an kashe kudaden da aka ware wa shirin tallafin karatu cikin hikima, domin daliban sun zarce yadda ake tsammani.

Ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na bunkasa ilimi nan gaba.

“Ziyarar ta ba ni damar yin hulɗa kai tsaye da ɗaliban, magance matsalolinsu da kuma tattara bayanai masu mahimmanci daga rukunin farko sama da ɗalibai 400 da aka ɗauki nauyin zuwa jami’o’i daban-daban a Uganda da Indiya, ” inji gwamnan.

A cewar sanarwar, ziyarar ta ba gwamnan damar gudanar da duba kai tsaye, wanda ya nufa inganta shirye-shiryen karbar masu cin gajiyar tallafin karatu na gaba, duka na kasashen waje da na cikin gida, domin tabbatar da kammala manufar 100:1 kafin karewar zangon gwamnatinsa na farko.

“Ziyarar gwamnan tana zama abin koyi ga dalibai domin su himmatu wajen samun nasarar ilimi, a gida da kuma kasashen waje,” in ji sanarwar.

Gwamna Yusuf ya ziyarci ɗaliban Kano da ke kan tallafin karatu a Indiya

NO COMMENTS