Gwamnatin Kano ta bukaci kwamitin harkokin yan sanda na majalisar wakilai karkashin shugaban kwamitin, Dan majalisa Abubakar Makki Yalleman ya rubanya kokari wajen kula da walwalar yan sanda domin inganta tsaron kasa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka ta bakin mataimakinsa kwamared Aminu Abdusalam Gwarzo, yayin ziyarar da kwamitin ya kai fadar gwamnatin Kano a Talatar nan.
Kwamitin yan sandan ya zo Kano ne domin duba aikin ginin makarantar sakandare ta yan sanda da ake yi a karamar hukumar Kabo.
Gwamnan ya bayyana damuwarsa game da yanayin tsaro, musamman a jihohin Arewa maso Yamma dake fama da ayyukan yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Kwamitin ya kuma gana da kwamishinan yan sandan jihar, Salman Dogo Garba a shalkwatar rundunar dake Bompai.
Shugaban kwamitin ya jaddada bukatar hadin kai tsakanin majalisar wakilai da rundunar yan sanda domin tabbatar da zamana lafiya.
Gwamnan Kano ya bukaci a kara kyautatawa yan sanda