SHARE

Gwamnatin Kano tace zata kara mayar da hankali wajen kyautata rayuwar malaman makarantun jihar musamman na firamare da sakandire domin samar da ingantaccen ilimi tun daga tushe.

Shugaban hukumar ilimin bai daya ta jihar nan Yusuf Kabir ne ya bayyana hakan bayan ya kare kasafin kudin hukumar na shekarar 2025.

Kabir yace a shekara mai kamawa ma’aikatar sa zata mayar da hankali wajen sauke dukkan hakkin malaman makarantun firamare da sakandiren jihar nan musamman ta bangaren albashin su da karin girma da samar da sabbin gine-gine domin habaka fannin na ilimi.

Shugaban hukumar daga nan sai yayi kira ga iyayen yara da duk masu ruwa da tsaki a fadin jihar Kano dasu bada cikakkiyar gudunmawar su domin samar da al’umma ta gari.

Shugaban hukumar ta ilimin bai daya yasha alwashin cigaba da aiwatar da tsare-tsaren gwamnatin Kano domin ciyar da ilimin Kano gaba.

Gwamnatin Kano ta jaddada aniyarta na kyautata rayuwar Malamai

NO COMMENTS