SHARE

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na samar da rumbunan ajiyar kayan aikin gona da taki mai inganci a dukkan kananan hukumomi 44 domin saukakawa manoma wahalar samun kayan aikin noma.

Shugaban kamfanin Samar da taki da kayan aikin noma (KASCO), Kabiru Sani Yakubu ne ya bayyana haka bayan ya Kare kasafin kudin kamfanin na shekara mai kamawa.

Yakubu, ya ce gwamnatin Kano ta yi gagarumin shirin wadata manoman Kano da wadatattun kayan aikin zamani da taki mai inganci kafin faduwar damunar badi a yunkurin gwamnatin na bunkasa fannin noma da wadata Kano da abinci.

Shugaban kamfanin na KASCO ya ce a shekarar da ake bankwana da ita, gwamnati ta yi wa manoman Kano ragin kaso hamsin cikin 100 akan takin zamani, wanda kuma suke sa ka ran saukakawa manoma a shekara mai  kamawa la’akari da yadda jihar Kano da najeriya baki daya suke cikin halin bukatar wadatuwar abinci.

Shugaban ya sha alwashin cewa damuna mai zuwa manoman Kano zas u yi farin ciki da tsarukan da gwamnati ta bijiro dasu domin yin noma cikin kwanciyar hankali.

Gwamnatin Kano za ta gina rumbunan ajiyar kayan gona – KASCO

NO COMMENTS