Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani kwamiti na musamman da zai bayar da shawarar yadda za a samar da bankin matasa na kasa.
Wannan wani bangare ne na a kokarin gwamnatin tarayya na karfafawa matasa gwiwa, hadi da tallafa musu ta hanyar da za ta samar da sauyi mai dorewa gare su.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai da hulda da jamaa na ma’aikatar ci gaban matasa Omolara Esan, ya ce Ministan matasan Kwamared Ayodele Olawande ne ya bayyana hakan a Abuja yayin da yake jawabi ga yan kwamitin a wani takaitaccen bikin kaddamarwa.
Ya ce aikin yan kwamitin shi ne jagorantar kafa bankin matasa, da fitar da tsarin tafiyar da harkokin bankin, nauoin ayyukan kudi da zai bayar da kuma yadda zai yi hulda da matasa.
Ya kuma jaddada cewa kwamitin zai mayar da hankali ne wajen ganowa da kulla alaka da cibiyoyin hada-hadar kudi da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa bankin matasa ya samu tallafin da ake bukata don fadadawa da cimma manufofinsa sannan kuma ya himmatu wajen samar da yanayin da zai tafi da kowane matashi ba tare da kallon matsayinsa ba.
Gwamnatin Tarayya ta fara kokarin samar da bankin matasa