SHARE

Dubban alummar dake aiki a masana’antar sarrafa robobi dake yankin unguwar Dakata a jihar Kano sun koka bisa yanda rashin wutar lantarki ke kawo nakasu ga sana’arsu.

Inda suka zargin kanfanin rarraba wutar lantarki na Kano KEDCO da hana su wutar lantarkin da gangan.

Ma’aikatan sun shafe kimanin watanni uku basa samun wadatacciyar wutar lantarki, wadda ita ce kaso 90 na dogaron kamfanonin wajen gudanar da ayyukan su.

Malam shamsuddin Aliyu, wanda shine mataimakin shugaban kungiyar ƴan kasuwa dake kasuwanci a masana’antar ta Dakata Small Scale, yace jihar Kano ce take kan gaba a cikin jihohin dake sarrafa robobi a kasarnan, amma sakamakon rashin wutar lantarkin ya janyo wa jihar ta koma baya.

Masu masana’antar sunce sun zauna da kamfanin na Kedco, domin samar da masalaha amma tafiyar bata sauya zani ba.
Kawo yanzu dai Kamfanin na KEDCO baiyi martani ba akan wannan zargin.

Masu kananan masana’antu a Kano sun koka bisa rashin wutar lantarki

NO COMMENTS