Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar Kaduna, ta dakatar da yajin aikin da ta tsunduma a kan mafi karancin albashi.
A ranar Litinin din da ta gabata ne kungiyar ta tsunduma yajin aiki sakamakon gazawar gwamnatin jihar wajen cika alkawarin da ta dauka na biyan mafi karancin albashi ga ma’aikata.
A zantawarsa da manema labarai, shugaban kungiyar reshen jihar Kaduna, kwamared Ayuba Magaji Sulaiman ya ce sun dakatar da yajin aikin ne sakamakon tattaunawa da suka yi da gwamnati.
Ya ce gwamnatin ta amince cewa akwai kura-kurai a tsarin da suka bi wajen biyan mafi karancin albashin tare da alkawarin za a gyara.
“Mun zauna da gwamnati kuma mun nuna musu kura-kuransu, sun kuma amince zasu gyara cikin mako guda, saboda haka nan da mako idan basu gyara ba to zamu cigaba,” inji shi.
Kwamared Ayuba yace a yanzu sun dakatar da yajin aiki amma idan gwamnati bata yi gyaran da ya kamata ba nan da mako guda zasu ci gaba.
NLC ya dakatar da yajin aiki a Kaduna