SHARE

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya amince da sama da Naira miliyan dari bakwai da talatin (N730,000,000) a matsayin tallafin karatu ga ‘yan asalin jihar Borno da ke karatu a cibiyoyin ilimi daban-daban a fadin kasar nan.

Kwamishinan Ilimi, Kimiyya, Fasaha, Engr. Lawan Abba Wakilbe, a hukumance ya mika kudin a madadin Gwamna Zulum ga hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Borno.

Engr. Wakilbe ya bayyana cewa, dalibai 26,888 ne za suci gajiyar tallafin idan aka kammala aiwatar da shi.

Hakazalika, ya bayyana cewar gwamnatin jihar ta kashe biliyan takwas akan tallafawa yan asalin jihar dake karatu a kasashen ketare.

Ya kuma yi karin haske kan kason kudin tallafin karatu, sannan ya bukaci daliban da su yi aiki tukuru domin tabbatar da irin dimbin jarin da gwamnati ke kashewa a fannin ilimi bai tashi a banza ba.

Zulum ya amince da Miliyan 730 don tallafawa karatun daliban jihar

NO COMMENTS