Membobi hudu na Majalisar Wakilai sun sauya jam’iyya daga Labour Party LP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress APC.
Shugaban Majalisar, Tajudeen Abbas, ya sanar da hakan a yayin zaman majalisar na Alhamis a dakin shuni na Majalisar Wakilai.
‘Yan majalisar na jam’iyyar Labour (LP) da suka sauya tafiya sun fito ne daga jihohi hudu: Kaduna, Imo, Edo, da Cross River.
‘Yan Majalisar sun hada da Chinedu Okere (Owerri Municipal/Owerri North/Owerri West), Mathew Donatus (Kaura ta Kaduna), Akiba Bassey ( Calabar Municipal/Odukpani) da Esosa Iyawe (Oredo ta Edo).
4 daga cikin ‘yan majalisar wakilai na LP sun koma jam’iyyar APC