SHARE

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ce addinin Musulunci bai haramta ilmin ‘ya mace ba.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a jihar Bauchi yayin kaddamar da shirin AGILE wanda Ma’aikatar Ilimi ta shirya tare da tallafin Bankin Duniya.

Taron, wanda aka gudanar da taken: “warware mastalolin Al’ada da Na Zamani kan Ilimin ’Ya’ya Mata a Yankin Arewa Maso Gabas: Muhimmancin Gudummawar Sarakuna da Malaman Addini,” ya jawo hankalin shugabannin gargajiya da na addini kan muhimmancin ilimin mata.

Sarkin Musulmi ya ce; “Musulunci bai haramta wa ’ya’ya mata neman ilimi ba, dalilai da dama ne ke haddasa wannan matsalar a wasu jihohi.. amma za a iya magance ta idan ana wayar da kan mutane”

Yace; “Lokacin da nake kan hanyata zuwa nan, na ga wasu yara suna talla a kan titi. Na tambaye su, suka ce suna zuwa makaranta ne da safe ko yamma a kan lokaci.

“Ina ganin yana da matukar muhimmanci mu duba kanmu da kyau. Ba abin da ya fi muhimmanci kamar bai wa ’ya’ya mata ilimi, domin hakan zai taimaka wajen inganta al’umma, don za ta kula da kanta, iyalinta da al’ummarta ba tare da la’akari da banbancin kabila ko addini ba.”

A jawabin sa, gwamnan jihar, Bala Mohammed ya ce gwamnatinsa na aiki tukuru don inganta ilimin mata a jihar.

Ya bayyana cewa tun daga lokacin da ya hau kan mulki a shekarar 2019, gwamnatinsa ta gina fiye da ajujuwan 5,000 tare da gyara wasu da dama.

Ya kuma yaba da rawar da sarakuna da malaman addini ke takawa wajen karfafa shiga, dorewa da kammala makaranta, musamman ga ’ya’ya mata.

 

Addinin musulunci bai haramta ilimin mace ba – Sarkin Musulmi

NO COMMENTS