SHARE

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya yi Allah wadai da satar shinkafa daga gonar gwamnati.

Gwamnan ya ce an saci adadi mai yawa na shinkafa daga gonar gwamnatin jiha da ke unguwar Jangwa a Karamar Hukumar Awe.

Gwamna Sule ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin karbar wata tawaga daga al’ummar Azara, karkashin jagorancin Sarkin Azara, Dr. Kabiru Ibrahim, a gidan gwamnati da ke Lafia.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim Addra, ya fitar, gwamnan ya nuna takaicin sa kan satar, yana mai bayyana lamarin a matsayin cikas ga yunkurin gwamnatin jihar na inganta samar da abinci da bayar da tallafi ga mazauna jihar.

“Akwai takaici s irin satar nan, musamman a lokacin da muke yin duk mai yiwuwa don kawo sauki ga mutanenmu da tabbatar da tsaron abinci a Nasarawa da wajen ta,” inji shi

Ya gargadi wadanda ke da hannu a lamarin da su daina irin wadannan miyagun dabi’u.

Gwamna Sule ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta dauki matakan da suka dace kan duk wanda aka kama yana sata daga gonar.

Barayi sun sace abinci daga gonar gwamnatin jihar Nasarawa

NO COMMENTS