SHARE

A yau Alhamis 5 ga watan Disamba, Dattijon Kasa Alhaji Tanko Yakasai ya cika shekaru 99 a duniya.

Alhaji Tanko Yakasai wanda dan jihar Kano ne, ya taka muhimmiyar rawa wajen karbowa Najeriya yancin kai daga Turawan Ingila, kuma guda ne daga cikin mutane da suka kafa jam’iyyar NEPU.

Ya rike mukamai daban daban da suka hada da kwamishinan yada labarai na Kano a shekarar 1967 zuwa 1971.

Ya kuma rike mukamin mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin majalisar dokoki a shekarar 1979 zuwa 1983.

Ya samu lambar girmamawa daga gwamnatin tarayya ta OFR da sauran lambobin yabo daga Kungiyar Yan jaridu ta kasa, Gidan Talabijin na kasa NTA, da makamantan su.

Tuni aka fara aikewa da sakon tayin murna ga Datiijo Alhaji Tanko Yakasai, ciki har da sakon shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, kamar yadda sanarwar mai taimakwa shugaban kasa kan yada labarai Bayo Onanuga ta nuna.

Dattijon kasa, Tanko Yakasai ya cika shekaru 99

NO COMMENTS