Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Brig. Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) ya ce an kama mutum dubu 14, 480 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi tsakanin watan Janairu zuwa Oktoban 2024.
Marwa, wanda ya bayyana hakan jiya Laraba yayin da ya ke zantawa da mambobin kwamitin majalisar wakilai kan yaki da ta’ammuli da miyagun kwayoyi, wadanda su ka kai ziyarar aiki a shalkwatar hukumar da ke Abuja.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne da hannu wajen safarar nau’ikan miyagun haramtattun kwayoyi kimanin kilo miliyan 2.4 a tashoshin jiragen ruwa, filayen jirgin sama, iyakokin kasa da kuma cikin gundumomi a fadin kasar.
Yayin da yake yabawa ‘yan majalisar kan goyon bayan da suka ba su, Marwa ya bukace su da su ci gaba da taimaka wa ayyukan hukumar domin cimma nasara.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin majalisar kan yaki da ta’ammuli da miyagun kwayoyi, Abass Adigun, ya yabawa shugabanni da ma’aikatan hukumar bisa jajircewarsu wajen gudanar da ayyukansu duk da kalubalen da suke fuskanta.
NDLEA ta kama mutum 14,480 bisa zargin safarar miyagun kwayoyi