SHARE

Majalisar Dattawa ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin Shugaban marasa rinjaye, Sanata Abba Moro (Benue ta Kudu) da zai gana da Babban Lauyan Tarayya (AGF) a yau, domin shawo kan matsalolin da ke da nasaba da kudurin sake fasalin haraji.

Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Barau I. Jibrin (Kano ta Arewa), wanda ya jagoranci zaman majalisar ya bayyana cewa majalisar dattawa da AGF za su gana a yau Alhamis a Abuja.

Sanata Barau ya ce za a ba wa dukkan bangarorin damar tofa albarkacin bakinsu wanda taron zai kai ga cimma matsaya mai ma’ana.

Baya ga Sanata Moro wanda shi ne shugaba, sauran mambobin kwamitin da za su tattauna da AGF a yau sun hada da: Tahir. Monguno (APC, Borno North), Muhammadu Aliero (PDP, Kebbi Central), da Seriake Dickson (PDP, Bayelsa West).

Sauran su ne: Titus Zam (APC, Benue North West), Abdullahi Yahaya (PDP Kebbi North), Adeola Olamilekan. (APC, Ogun West), Sani Musa (APC, Niger East) da Adetokunbo Abiru (APC, Legas Gabas).

Majalisar dattijan ta yiwa kudurin gyaran harajin karatu na biyu a makon da ya gabata, kuma ta mika shi ga kwamitinta kan harkokin kudi domin ci gaba da aiki akanshi, bayan da ta samu bayanai daga shugaban kwamitin shugaban kasa kan manufofin kasafin kudi da sake fasalin haraji, Taiwo Oyedele, shugaban hukumar tara haraji ta kasa. (FIRS), Zacchaeus Adedeji; da Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kudi, Tanimu Yakubu.

Sai dai a jiya Majalisar Dattawa ta bukaci kwamitin kudi da Sanata Musa ya jagoranta da kada ta shirya taron jin ra’ayin jama’a ko kuma ta ci gaba da bin tsarin doka kan kudirorin har sai an kammala ganawar da AGF.

Barau, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya ce, “Kafin gabatar da wadannan kudirori, mun san mun fuskanci matsaloli da dama da muka yi ta kokarin magancewa.

“Mun kuma amince da cewa kada mu bar wani abu ya kara ta’azzara matsalolin kasarmu. A kan haka ne hukumar zartaswa da kuma mu suka amince da cewa a samar da wani taron da zai zauna da babban lauyan gwamnatin tarayya domin mu magance duk wadannan matsaloli domin amfanin al’ummar kasar nan.”

Yan majalisa zasu tattauna da babban lauyan kasa akan kudurin gyaran haraji

NO COMMENTS