SHARE

Rundunar yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da harin da yan bindiga suka kai wa mahaifiyar gwamnan jihar da kanwarsa.

An samu rahoton kai hari kan mahaifiyar Agbu Kefas,, Jummai Kefas da kanwarsa mai suna Atsi Kefas a titin Kente a karamar hukumar Wukari.

Kakakin rundunar, Usman Abdullahi ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Juma’a, kamar yadda reshen rundunar a Wukari ya tabbatar masu.

Ya bayyana cewa sun samu rahoton yan fashi da makami sun kai hari kan matafiya a hanyar, amma ba a sanar da su cewar dangin gwamnan jihar ba ne.

“Ana binciken lamarin, kuma ana sa ran hukunta wadanda su ka tafka wannan danyen aiki,” inji shi.

Kawo yanzu, gwamnan jihar bai ce komai a kan lamarin ba a hukumance, amma sakataren gwamnati, Timothy Kataps ya ta bayyana labarin a matsayin labarin karya.

Amma wasu daga cikin iyalan gwamnan da su ka nemi a boye sunansu, sun tabbatar da harin, kuma an bayyana cewa ana duba lafiyar mahaifiyar gwamnan.

Yan bindiga sun kai gari mahaifiyar gwamnan Taraba

NO COMMENTS