Kotun shari’ar addinin musulunci dake Shahuci a Kano , karkarkashin Mai Shari’a Abdu Abdullahi Waiya, ta raba auren, Taslim Baba Nabegu da kuma mijinta Nasir Buba ( Jalam) a ranar Juma’a .
Tunda farko, matar ta garzaya gaban kotu ne, inda ta yi karar mijinta don neman saki tunda ba za ta iya ci gaba da zama da shi ba.
A baya lauyan Nasir Buba, Barista Saluhu Umar Kududdufawa, ya roki Kotun ta maida da Shari’ar zuwa wata kotun.
A zaman kotun na ranar Juma’a, babu wanda ya halacci zaman, kuma babu wani aike kan dalilin rashin bayyanarsu a gaban kotun.
Alkalin kotun, Mai shari’a Malam Abdu Abdullahi Waiya, ya ce sun raina kotun , inda ya kafa hujjojin yanke hukuncin sakin matar ta hanyar kuli’i, da za ta biya tsohon mijin nata Naira miliyan daya.
Hukuncin na zuwa ne, bayan wani zargi da tsohon mijin ya yi wa tsohuwar matar tasa na mu’amala da wani kwamishina a jihar Jigawa, abinda ya ja hankali matuka a jihar Kano.
Kotu ta raba auren Taslim da Mijinta ta hanyar kul’i