Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, sun nuna alhininsu kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Muyideen Ajani Bello, wanda ya rasu ranar Juma@ yana da shekaru 84.
A wata sanarwa da mai baiwa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a, Tinubu ya bayyana mutuwar malamin a matsayin babban rashi ga al’ummar Musulmi da ƙasa baki ɗaya.
“Sheikh Muyideen Ajani Bello mutum ne mai zurfin fahimta kan Alƙur’ani mai girma. Fassarorinsa sun kawo sauƙi da jagoranci ga miliyoyin mutane,” in ji Tinubu.
Ya ƙara da cewa, “Yin ibada da nazari mai zurfi a farkon rayuwarsa ya gina kyakkyawar makoma ga Musulmai a Najeriya da ma ƙetare.”
Shugaban ya yaba wa malamin kan faɗakarwarsa kan sadaqa, zaman lafiya, da adalci.
Ya ce, “Sheikh Bello ya kasance yana jan hankalin shugabanni su kasance masu gaskiya, rikon amana, da adalci a mulkinsu.”
Tinubu ya roƙi Allah ya gafarta masa, ya ba shi Aljanna Firdausi, tare da yiwa iyalansa da al’ummar Musulmi addu’ar samun haƙuri. Har ila yau, ya bukaci ‘yan Najeriya su yi koyi da kyawawan halayen marigayin.
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, tare da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, sun kasance cikin wadanda suka yi jimami kan wannan babban rashi.
Sanwo-Olu ya ce, “Rasuwar Sheikh Bello babban rashi ne ga jihar mu da al’ummar Musulmi gaba ɗaya. Allah ya gafarta masa, ya sa Aljanna ce makomarsa.”
Tinubu da Gwamnoni sun yi jimami kan rasuwar sheikh Muyideen Bello