SHARE

Gwamnatin Jihar Benue ta sanar da shirin sake sanya sunan Jami’ar Jihar Benue da ke Makurdi domin girmama wanda ya kafa ta, tsohon gwamna marigayi Rev. Fr. Moses Adasu.

Gwamna Hyacinth Alia ya sanar da shirin sake sanya sunan Jami’ar Jihar Benue a ranar Asabar yayin bikin yaye dalibai da aka gudanar a harabar jami’ar.

Ya bayyana cewa an gabatar da kudiri na musamman ga Majalisar Dokokin Jihar Benue domin amincewa da sauyin sunan. Idan aka amince, jami’ar za ta zama Reverend Father Moses Adasu University.

Marigayi Rev. Fr. Moses Adasu, wanda ya kasance firist na Katolika kuma gwamnan Jihar Benue daga 1991 zuwa 1992, ya kafa Jami’ar Jihar Benue a matsayin wani muhimmin ɓangare na gado da nufin inganta samun damar ilimi a jihar.

Gwamna Hyacinth Alia, yayin jawabinsa a bikin yaye dalibai, ya ce, “Don girmama wanda ya kafa wannan jami’ar, gwamnatina ta tura kudirin zartarwa ga majalisar dokoki don jami’ar ta samu sunan wanda ya kafa ta, Rev. Fr. Moses Adasu.”

Baya ga shirin sake sanya sunan jami’ar, Gwamna Hyacinth Alia ya sanar da kafa sabuwar cibiyar jami’a a Adikpo, karamar hukumar Kwande. Wannan matakin na da nufin kara samun damar ilimi ga mazauna yankin Benue North East Senatorial District.

Gwamna Alia ya bayyana dalilin da yasa ake neman sauya sunan Jami’ar Benue

NO COMMENTS