Rundunar yan Sandan jihar Kano, ta samu nasarar kama miliyoyin Dalolin kasar Amurka da Naira da kuma sauran kudaden ketare, da Ake zargin na bogi ne don cutar da ƴan kasuwa.
Mai magana da yawun rundunar ƴan Sandan jijar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga Freedom Radio Kano, a ranar Lahadi 8 ga watan Disamba 2024.
Rundunar ta ce yanzu, mutanen da ake zargi da kuma makudan kudaden suna hannunsu, kuma ci gaba da lissafa su.
SP Kiyawa, ya ja hankalin ƴan kasuwa, da su ƙara sa ido a kan dukkan kudaden da ake kawo mu su don kaucewa fada tarkon mayaudara.
”Yan kasuwa a kara sa ido, irin wadannan mutanen da muka kama da kudade a wajensu, ba su kadai ba ne, duk wanda ya zo siyayya da makudan kudade na farko a samu kwararru su duba kudin musamman wadanda suke canja Dala,” cewar SP Abdullahi Kiyawa.
Rundunar ƴan sandan ta kara da cewa, zargin da suke yi shi ne za a dinga shigar da kudaden bogin da kaɗan-kaɗan zuwa kasuwanni.
A karshe, rundunar ta ce ta na ci gaba da gudanar da bincike, kuma ba za ta gajiya ba wajen ci gaba da wayar da kan al’umma daga wannan almundahana.
Yan sandan sun cafke mutanen da ake zargi da safarar Dalolin bogi zuwa Kano