A yau Litinin, wasu ‘yan daba sun kai farmaki harabar Babban kotun Jihar Edo da ke Benin, da nufin dakile zaman sauraren karar rikicin sakamakon zaɓen gwamna na ranar 21 ga watan Satumba.
Zaɓen, wanda ya bai wa Monday Okpebholo na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) nasara, jam’iyyun adawa guda bakwai ke kalubalantarsa.
Magoya bayan jam’iyyun adawar sun kasance a kotun lokacin da wasu mutane da ba a san ko su waye ba suka kai musu hari a wajen kotun.
Jami’an tsaro sun gaggauta ɗaukar mataki, inda suka toshe kofar shiga kotun tare da kafa shingen bincike a kan hanyoyin zuwa kotun.
Kawo yanzu dai babu wata sanarwa daga rundunar yansandan jihar, kan wadanda ake zargi da kai harin.
Batagari sun kai hari kotun sauraren kararakin zaben gwamnan Edo