SHARE

Gwamnatin Tarayya ta bayyana wani jerin sunayen jakadun kasarnan a ketare dake yawo a shafukan sada zumunta a matsayin na bogi.

Mukaddashin mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Ma’aikatar tana mayar da martani ne kan rahotannin da ke cewa gwamnatin ta fitar da jerin sunayen jakadun da za a nada.

Sanarwar ta fayyace cewa hakkin shugaba Bola Tinubu ne ya nada jakadu, wanda kuma har yanzu bai yi ba.

Ma’aikatar ta kara da cewa ya kamata jama’a su yi watsi da ikirarin an nada wadanda ke cikin wannan jerin sunayen.

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da bata fitar da jerin sunayen jakadun da zata nada ba

NO COMMENTS