Gwamnatin tarayya ta ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta ɗauki batun samar da abinci a matsayin muhimmin abu.
Karamin ministan noma da samar da wadatar abinci, Aliyu Abdullahi, ya sanar da haka.
Ya ce tun bayan rantsar da shugaba Tinubu a watan Mayu 2023, gwamnati ta ƙaddamar da shirye-shirye don tabbatar da wadatar abinci a ƙasar.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana matuƙar damuwa game da yanayin wadatar abinci. Sau da yawa yana gaya mana cewa burinsa shi ne mu kai Najeriya ga matsayin da babu wanda zai kwanta da yunwa.”
“Mun fahimci wannan, kuma muna aiki tukuru don tabbatar da mun cimma hakan,” in ji Abdullahi.
Farashin abinci ya ƙaru sosai a cikin ƴan shekarun nan, wanda ya sa abinci ya fi ƙarfin miliyoyin mutane.
Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi sun ɗauki matakai daban-daban don rage wannan matsalar, ciki har da rabon tallafi ga miliyoyin ‘yan Najeriya.
A bara – watanni kaɗan bayan ya hau mulki – Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkar abinci.
“Kar ko dan Najeriya 1 ya kwana da yunwa,” Minista ya fadi manufar Tinubu