SHARE

Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta ƙara kaimi wajen yaƙi da amfani da sinadarai masu haɗari a cikin burodi a fadin Najeriya.

Hukumar ta bayyana cewa irin waɗannan sinadarai sun haɗa da saccharin da bromate, inda ta sake jaddada gargaɗi mai tsanani ga masu yin burodi kan amfani da irin waɗannan abubuwan, saboda haɗarin da suke haifarwa ga lafiyar jama’a.

Da take magana a wani taron manema labarai, darakta-janar ta hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta tabbatar da aniyar hukumar na kare lafiyar jama’a ta hanyar sa ido kan kayayyaki dake shiga kasuwa.

“Sa idonmu kan kayayyakin dake shiga kasuwa yana da matuƙar muhimmanci wajen tsaron lafiyar jama’a,” inji Farfesa Adeyeye,

inda ta ƙara da cewa, “Muna yawan duba kayayyaki a kasuwa, kuma muna ɗaukar mataki bisa ga korafe-korafen da ake aiko mana ta ofishin mu.”

Baya ga burodi, NAFDAC tana kuma tsananta matakin da take ɗauka kan wuraren samar da ruwan sha, tana rufe waɗanda ba sa cika ka’idojin tsafta da inganci.

Daraktar tace suna Kula domin tabbatar da cewa kayayyakin da ke kasuwa suna bin tsare-tsaren da aka amince da su a lokacin rajista.

Sai dai ta nuna takaicinta game da gano cewa wasu masu masana’antu suna canza tsarin sinadaran kayayyakin su bayan rajista, wanda hakan ya sanya su matsawa sosai domin tabbatar da bin ka’idoji na lafiya.

Farfesa Adeyeye ta jaddada mahimmancin kula da kayayyaki a kasuwa wajen tabbatar da bin ka’idoji da kuma kare masu amfani da kayayyaki daga abinsa kaje yazo sakamakon amfani da kayan da suka lalace.

NAFDAC ta gargadi masu burodi

NO COMMENTS