Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume, ya bukaci jiga-jigan siyasar Arewa masu shirin takara a zaben 2027 su Dakatar zuwa 2031 bayan shugaba Tinubu ya gama wa’adin mulki a karo na biyu.
Akume ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da ya kawar da tunanin karbar mulkin shugaban kasa a 2027, inda ya ce idan Allah ya nufa ya zama shugaban kasa zai iya lashe zabe yana da shekaru 90 a duniya.
Ya bayyana hakan a wani shirin gidan talabijin na TVC kan harkokin siyasa, ya ce har yanzu lokaci ne na Kudu ta jagoranci kasarnan.
Akume ya ce shugaba Tinubu bai rasa goyon bayan ‘yan Najeriya ba, sakamakon kudirin gyara haraji da sauran tsare-tsare na tattalin arziki da ya dauka a cikin watanni 17 na gwamnatinsa, ya kuma bayyana fatansa na cewa shugaban kasar ne zai tafiyar da Najeriya na tsawon shekaru 8.
Ya kare kudirin sake fasalin haraji a matsayin wasu tsare-tsare masu kyau da za su taimaki kasar nan idan Majalisar Dokoki ta kasa ta amince da su.
Ya ce,“Ya kamata a bar Shugaba Tinubu a matsayinsa na dan Kudu ya karasa wa’adi biyu, saboda haka Yan Arewa su dauke idonsu daga kan kujerar”
Yan Arewa su kauda idonsu daga shugabancin kasa sai 2031 – George Akume