SHARE

Kungiyar tuntuba ta Arewa, da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, da sauran masu ruwa da tsaki sun caccaki fadar shugaban kasa kan ikirarin cewa shugaba Bola Tinubu zai ci gaba da mulki har 2031.

ACF ta ce kamata yayi Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali kan samar da cigaban kasa maimakon batun zaben 2027.

DAILY POST ta rawaito sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya tayar da kayar baya a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da ya bukaci jiga-jigan siyasar arewacin kasar da ke shirin tsayawa takarar shugabancin kasar a 2027 da su dakata su jira har zuwa 2031 lokacin da Shugaba Tinubu zai kare wa’adinsa na biyu.

Sai dai kuma da yake mayar da martani kan kalaman Akume, Sakataren Yada Labarai na ACF na kasa Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ya bayyana cewa yayi wuri a fara cecekuce akan zaben 2027.

Mohammad-Baba ya jaddada cewa ACF bata da wata matsaya akan wanda ya kamata ya jagoranci kasar a zabe mai zuwa.

Hakazalika ya jaddada cewar tayarda wannan zancen kawai hanya ce ta dauke hankalin al’umma daga abubuwan da suke faruwa a kasar.

A nasa bangaren Atiku yace akwai gibin akalla Shekaru shida tsakanin adadin lokacin da arewa da kudu suka shafe suna mulkar kasarnan.

Atiku a jawabin da mai taimaka masa a fannin yada labarai Paul Ibe ya fitar yace ikon zaben shugaba tana hannun yan kasa, su ya kamata suyi nazarci su gani “Shin gwamnatin Tinubu tayi abunda ya dace da ya kamata ta zarce wa’adin na biyu? Abun takaici gwamnatin Tinubu ba zata iya bugar kirgi tace tayi abunda ya dace ba”

ACF da Atiku Abubakar sunyi martani kan batun Akume cewar Arewa ta dauke idonta daga zaben 2027

NO COMMENTS