SHARE

Shahararren dan siyasar nan daga jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya zargi jam’iyyar APC ta shugaba Bola Tinubu da mallake wasu jam’iyyun siyasa.

Galadima ya ce, Tinubu yana son sabbin jam’iyyun su yarda da manufofinsa domin kar a samu wanda zai kalubalanci shi a zaben 2027.

Galadima ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da aka yi da shi a shirin News Night na Arise Tv.

Galadima ya ce: “Mun san a yau cewa wannan gwamnatin APC na tura wakilai domin su yi musayar ra’ayi da shugabannin jam’iyyun siyasa, suna bayar da biliyoyin naira ga shugabannin jam’iyyun.”

“Sun kuma yi alkawarin cewa dukkan jam’iyyun siyasa sai sun goyi bayan manufofin wannan gwamnati domin a shekarar 2027, ba za a samu wanda zai kalubalance su ba.”

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su tabbatar da ingantaccen zabe.

“Ina matukar farin cikin cewa, ta hanyar akwatin zabe, ‘yan Afirka na iya sauya gwamnati.

“Dole ne dukkanmu mu tashi tsaye domin tabbatar da cewa abin da ke faruwa a kasarmu yana cikin tsari, ba don ‘yan siyasa kawai ba,” in ji shi.

Wannan zargi na Galadima na zuwa ne bayan da Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, George Akume, ya gargadi tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, da shugabannin siyasar Arewa daga neman takarar shugaban kasa a 2027.

Akume ya ce Atiku da Arewa su bai wa Tinubu su hakura da tunanin mulkar Najeriya har sai bayan 2027.

Buba Galadima ya zargi APC da kokarin mallake ‘yan adawa

NO COMMENTS