SHARE

Gwamnan Jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda, ya kaddamar da aikin gina titin Kofar Soro-Kofar Guga Roundabout wanda ya kai naira biliyan 3.5 a cikin birnin Katsina.

Gwamnan ya bayyana cewa titin, wanda aka kaddamar da shi a ranar Litinin, wani ɓangare ne na shirin sabunta birane na gwamnatin sa, wanda ke nufin inganta hanyoyin ababen more rayuwa a jihar.

Radda, yayin kaddamar da aikin, ya bayyana cewa gwamnati ta kuduri aniyar samar da wuraren birane na zamani da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.

Haka kuma, ya bayyana cewa zuba jari a cikin muhimman ababen more rayuwa, kamar gina hanyoyi, yana taimakawa wajen kafa tubalin ci gaban dorewa na Katsina.

Gwamnan Katsina ya kaddamar da aikin hanyar naira biliyan 3.5

NO COMMENTS