Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa akalla ‘yan Najeriya 10,000 ne aka tsare bisa laifukan karya dokokin shige da fice a kasashen Afirka da kasashen Turai a bana.
Sai dai ya yaba da irin gudunmawar da bakin haure ‘yan Najeriya ke bayarwa ga tattalin arzikin duniya, inda ya ce Najeriya ce ke kan gaba a yawan kudaden da ‘yan cirani ke samarwa a yammacin Afirka.
Baya ga kudaden da ‘yan kasashen ketare ke fitarwa, ya ce ‘yan ci-ranin Najeriya sun zama jakadun na gari a fadin duniya wadanda suka yi fice a fannin fasaha, likitanci, wasanni, kere-kere da sauransu.
Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan jawabi a ranar Litinin yayin taron tattaunawa na shekara-shekara karo na 10 akan hijira zuwa wasu kasashen a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Ya ce, “Hijira tana da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa da ma duniya baki daya. A shekarar 2022 kadai, ‘yan Najeriya dake ketare sun samar da kdalar Amurka biliyan 21.9.”
Ya kara da cewa Najeriya kasa ce dake maraba da bakin haure inda sama da bakin haure miliyan 1.3 ke zaune a kasarnan sai dai ya yi gargadi game da kalubalen da ake fama da shi na hijira ba bisa ka’ida ba.
Yace a kalla an dawo da ‘yan Najeriya 10,000 da aka samu da karya ka’idar haraji data kasashe daban daban a shekarar 2024.
Yan Najeriya 10,000 aka samu da karya ka’idar shige da fice a bana -Kashim Shettima