Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta sanar da nasarorin da ta samu a kan masu aikata laifuka, ciki har da kashe ɗan bindiga, hana yunkurin yin garkuwa da mutane, da kuma kama wasu mutum uku da ake zargin masu fashi da safarar makamai ne.
Kakakin rundunar, ASP Mansir Hassan, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa, ya ce an kuma kwato bindigogi da alburusai a yayin hare-haren da aka kai tsakanin 8 zuwa 10 ga Disamba, 2024, da taimakon bayanan sirri da aka samu.
A cewarsa, a ranar 8 ga Disamba da misalin ƙarfe 2:45 na safe, jami’an daga reshensu da ke Kasuwan Mata sun kama wani mutum ɗan shekara 35 mai suna Adamu Yahaya a wani wata mashaya da ke Zariya. An same shi da bindigar da aka ƙera a gida, harsashi ɗaya, da kuma ankwa.
Hassan ya ce, “A wani aikin da aka gudanar a wannan rana, tawagar sintiri daga sashen Barnawa ta kama wasu mutane biyu, Andrew Emmanuel da Mendwas Peter Bulus, yayin bincike a hanya. An kwato bindiga, wayoyi biyu na Infinix, da kuma ƙwayar wiwi. Wadanda ake zargin sun amsa cewa suna da hannu a fashin makami a Kaduna, kuma bincike na ci gaba don gano sauran ‘yan tawagarsu.”
Ya ƙara da cewa, “A ranar 9 ga Disamba, wata tawagar sintiri daga sashen Dan Magaji ta kama mutane uku a kan babbar hanyar Kano-Kaduna. An gano harsashi 216 na 9mm da harsashi guda ɗaya na 7.62x39mm a wajen Buhari Suleiman, Jamil Yakubu, da Aliyu Abdullahi, ana zaton suna da hannu a safarar makamai. Bincike ya nuna Yakubu ya sayi harsashi daga Suleiman kafin a kama su.”
A ranar 10 ga Disamba, DPO na sashen Damakasuwa tare da haɗin gwiwar KADVS da CJTF sun dakile wani hari na ‘yan bindiga kan mazauna Tudu Gishere. An kashe ɗan bindiga guda ɗaya yayin da sauran suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ibrahim Abdullahi, ya yaba wa jami’an bisa jajircewarsu kuma ya yi kira ga mazauna jihar su rika bayar da bayanai cikin lokaci da na gaskiya don taimaka wa yaƙi da aikata laifi a Kaduna.
‘Yan sanda a Kaduna sun kashe ɗan bindiga