SHARE

Jamiyyar APC ta yi martani da cewa hadakar tsohon mataimakin shugaban kasar nan Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi ta yi kadan ta iya tasirin kawar da shugaban Tinubu a matsayin shugaban kasa a karo na biyu a zaben 2027.

Daraktan yada labarai na jamiyyar APC na kasa, Bala Ibrahim ne ya yi wannan martani a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Punch a ranar Talata.

Bala Ibrahim yana mayar da martani ne ga wata sanarwa da mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya fitar da ke cewa shugaban nasa da takwaransa na jam’iyyar Labour sun koyi darasi a zaben da ya gabata kuma za su hada kai don korar gwamnatin APC wadda ke cike da rashin kwarewa wajen iya shugabanci.

A cewarsa, idan aka hada kuriun shugabannin biyu da za su kai miliyan 12, zata kawo karshe zarcewar Tinubu a Karo na biyu tare da kawar da wahalhalun da jamiyyar APC ta kakabawa yan Najeriya.

Hadin gwiwwar Atiku da Obi tayi kadan ta kawar da Tinubu daga kan mulki a 2027 – APC

NO COMMENTS