Hukumar Kula da Harkokin Sarrafawa da Tacewa da Sufurin Man Fetur a Nijeriya, (NMDPRA) ta gargadi ‘yan kasuwar man fetur kan boye mai da kuma duk wani abu da zai cutar da jama’a yayin bukukuwan karshen shekara.
Hukumar ta kuma gargadi mazauna jihar Osun da su guji sayen mai fiye da kima da kuma boye man fetur a gidajensu.
Mr. Kunle Adeyemo, mai kula da hukumar NMDPRA a jihar, ya yi wannan gargadin ne yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Osogbo.
Adeyemo ya bayyana cewa duk wani dan kasuwa da aka kama yana boye mai ko kuma yana yin tauye ma’auni, zai fuskanci hukunci.
Shugaban NMDPRA ya kuma ce jami’an hukumar za su ci gaba da zagayawa a fadin jihar domin gudanar da sintiri da sa ido tare da daukar mataki kan duk wani dan kasuwa da aka samu da laifi.
A cewarsa, NMDPRA a jihar za ta kara kaimi wajen gudanar da sa ido da sintiri a tashoshin mai, bisa tanadin dokar hukumar, domin tabbatar da bin ka’idoji kan inganci, adadin mai da kuma tsaron ayyuka.
Adeyemo ya kuma gargadi masu motoci da su guji sayen mai fiye da kima da kuma boye man fetur a ciki ko kusa da wuraren gidajensu domin kaucewa haddasa gobara.
NMDPRA ta gargadi masu boye man fetur