SHARE

Ƙotun sake sauraron shari’a tsakanin Hukumar Karbar Korafe Korafe da Hana Cin Hanci da rashawa ta Jihar Kano da tsohon Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da Sauran Mutane 6 ta dage shari’ar zuwa ranar 13 ga watan janairu na 2015

Mai shari’a Amina Adamu Aliyu Itace ta sanar da hakan a zaman kotun da ya gudana a Jiya Laraba wanda aka tafka mahawara a tsakanin bangarorin dake kare wadanda suke wakiita.

Mai shari’ar ta kuma umarci Lauyoyin bangarorin biyu da suyi taka tsan tsan da kalaman da zasu furta a gaban kotu.

Hukumar Karbar Korafe Korafe ta Jihar Kano dai ta Gurfanar da Dr Abdullahi Umar Ganduje da Mai dakinsa Dr Hafsat Ganduje da Kuma Umar Abdullahi Ganduje Sai Abubakar Bawuro, da Jibrilla Muhammad, sai Kamfanin Lamash Properties Limited, da Safari Textiles Limited, sai Lasage General Enterprises Limited.

Kotu ta daga sauraron shari’ar Ganduje zuwa 13 ga watan Junairu

NO COMMENTS