Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin Farfesa Shehu Galadanci a matsayin Shugaban Kwamatin Shura na Kano.
A wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, ya bayyana cewa Gwamna Abba ya kuma nada tsohon Shugaban Ma’aikata na Fadar Gwamnatin Kano, Alhaji Shehu Wada Sagagi, a matsayin Sakataren Kwamatin.
Sanarwar ta ce: “Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Farfesa Shehu Galadanci a matsayin Shugaban Kwamatin Shura na Kano, tare da tsohon Shugaban Ma’aikata, Alhaji Shehu Wada Sagagi, a matsayin Sakataren Kwamatin.”
Har ila yau, Gwamnan ya amince da nadin mutum 46 da zasu zama mambobin kwamatin.
Sanarwar ta ce: “Mambobin kwamatin sun kunshi malamai, malaman jami’a, da sauran shugabannin al’umma, wadanda za su bayar da gudunmuwa wajen ci gaban Kano.”
Farfesa Sani Zaharadden ya zama Mataimakin Shugaban Kwamatin.
Gwamna Yusuf ya nada Farfesa Shehu Galadanci shugaban kwamatin shura na Kano