SHARE

Majalisar tattalin arzikin Najeriya ta karɓi rahotonnin matsayar gwamnonin jihohin ƙasar 36 kan kafa rundunonin ‘yansandan jihohi.

Majalisar tattalin arzikin ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, ta yi zamanta a jiya Alhamis a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja, inda gwamnoni da mataimakan wasu gwamnonin suka halarta tare da wasu masu bai wa shugaban ƙasa shawara.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnatin jim kaɗan bayan kammala ganawar, gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ce gwamnonin jihohin sun nuna cikakken goyon bayansu kan ƙirƙirar ‘yansandan jihohi saboda matsalolin tsaro da jihohin ke fama da su.

To sai da majalisar ta dakatar da tattaunawa game da batun har sai a zamanta na gaba da za a yi cikin watan Janairun sabuwar shekara mai kamawa.

Majalisar tattalin arziki ta karbi rahoton matsayar gwamnati kan kafa ‘yan sandan jihohi

NO COMMENTS