SHARE

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja zuwa Dubai, hadaddiyar D’daular larabawa, a ranar Juma’a, 13 ga Disamba, 2024, domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bikin kaddamarwa da sanya sunan wata cibiyar adana man fetur.

An yi kiyashin kashe akalla Dala miliyan 325 wajen samar da cibiyar.

Wannan cibiyar, mallakar kamfani mai zaman kansa na Najeriya, Oriental Energy Limited, za a kaddamar da ita a ranar 14 ga Disamba, 2024.

Bayan bikin kaddamarwar a Dubai, Mataimakin Shugaban Kasar zai wuce zuwa Saudiyya inda zai yi aikin Umrah daga ranar 16 zuwa 19 ga Disamba, 2024.

A ranar 20 ga Disamba, 2024, Shettima zai gudanar da taron tattaunawa na musamman tare da shugaban bankin raya kasashen Musulmi (IsDB) a birnin Jeddah.

Tattaunawar za ta maifa da hankali kan tsarin hadin guiwa wajen daukar nauyin shirin Special Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ Phase II) da kuma inganta gudanar da ayyukan IsDB a Najeriya, domin karfafa bunkasar tattalin arziki da aikin gona na kasar.

Ana sa ran Mataimakin Shugaban Kasar zai dawo Najeriya kafin ko a ranar 21 ga Disamba, 2024.

Mataimakin shugaban kasa, Shettima ya tashi zuwa Dubai

NO COMMENTS