Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Juma’a ya halarci daurin auren ‘ya’yan mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Barau Jibril, da Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero, a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin sadarwa na zamani, Dada Olusegun, ne ya bayyana hakan a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin X a ranar Juma’a.
A rubutun da ya yi, ya ce:
“Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya halarci sallar Juma’a da kuma daurin auren ‘ya’yan Sanata Barau Jibril (CFR), Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta 10, da Mai Martaba Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero (OFR), a Masallacin Ƙasa, Abuja.
Shugaba Tinubu ya halarci daurin auren ‘ya’yan Barau da Sarkin Bichi