Jam’iyyun PRP da ADC sun sanar da hadewa domin magance matsalolin da suka addabi Najeriya, ciki har da karyewar tsarin dimokuradiyya, matsalar tattalin arziki, da cin hanci da rashawa.
Jam’iyyun biyu sun bayyana wannan kuduri a taron manema labarai da suka gudanar a birnin tarayya Abuja ranar Juma’a, wanda ke zama wani sabon salo a siyasar Najeriya, gabanin zaben 2027.
Da yake jawabi, shugaban PRP na kasa, Dr. Falalu Bello, da shugaban ADC na kasa, Ralph Nwosu, sun yi bayani kan muhimmancin samar da hadin kai domin tunkarar kalubalen tabarbarewar lamura a kasa.
Sun soki halin da dimokuradiyyar Najeriya ke ciki, musamman kan batum adalci da gaskiya a tsarin zabe, tun bayan zaben 2023 da kuma zaben kananan hukumomi da ake gudanarwa yanzu.
Jam’iyyun sun yi kira da a yi garambawul ga tsarin zabe domin dawo da aminci a tsarin dimokuradiyya, suna mai jaddada cewa makomar kasar ta dogara ne ga zabe mai tsafta da gaskiya da kuma adalci.
A bangaren tattalin arziki, shugabannin PRP da ADC sun soki yadda tattalin arzikin kasar ke kara tabarbarewa, inda GDP ya ragu daga dala biliyan 493 a shekarar 2015 zuwa dala biliyan 352 a shekarar 2024.
Sun nemi sauya tsarin tattalin arziki zuwa tsarin da zai mayar da hankali kan samar da kayayyaki, ƙirƙirar ayyuka, da gyaran tsarin ilimi, musamman ga miliyoyin yara da basa zuwa makaranta.
Jam’iyyun Sun kuma bayyana cin hanci da rashawa a matsayin abinda ke cigaba da lalata tsarin siyasar kasar nan, suna bayar da misalin batun “ƙarin kasafin kuɗi” a Majalisar Dokoki ta Tarayya.
Sannan sai suka yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya ba tare da bambamcin kabila, addini ko siyasa ba da su shiga wannan gwagwarmaya.
Zaben 2027: ADC, PRP sun hade