Hukumomin kasar Finland sun rufe dukiyar Simon Ekpa, wanda ya ayyana kansa a matsayin mai rajin kafa kasar Biafra, wanda ke fuskantar zarge-zargen da suka shafi ayyukan ta’addanci.
A cewar jaridar Yle, wata kafar labarai ta kasar Finland, gwamnatin Finland ta kuma rufe kadarorin kamfanonin da ke da alaka da Ekpa da wasu mutum hudu da ake tsare da su.
Rahoton ya bayyana cewa Ekpa yana tsare a gidan yari na Kylmäkoski, wanda aka san shi da tsauraran matakai a duniya. An kafa gidan yarin a watan Janairu 1993 a gundumar Kylmäkoski.
A ranar 21 ga Nuwamba, ne aka tura Ekpa gidan yari bisa zargin yada labaran ta’addanci ta kafafen sada zumunta.
Wata kotun gundumar Päijät-Häme ce ta ba da umarnin tsare shi bayan hukumar binciken manyan kaifuka ta Finland (NBI) ta kama shi tare da wasu mutum hudu da ake zargi da aikata laifukan ta’addanci.
Ana zargin Ekpa, wanda ya ayyana kansa a matsayin Firayim Minista na gwamnatin Biafra Mai gudun hijira da aikata laifin ne a shekarar 2021 a gundumar Lahti.
Ana tuhumarsa da tada zaune tsaye da kuma ta da hankalin jama’a a Kudu maso Gabashin Najeriya ta kafafen sada zumunta.
An shirya fara shari’ar sa a watan Mayu na shekarar 2025.
Hukumomin Finland sun garkame mai fafutukar kafa Biafra, Ekpa a kurkuku