in

Jam’iyyar PRP ya zargi Tinubu da rusa tattalin arziki

Jam’iyyar PRP ta soki manufofin tattalin arzikin shugaba Bola Tinubu, tana zargin gwamnatinsa da rusa matsakaitan masu abin hannu a Najeriya.

Shugaban PRP, Bello Falalu, ya yi wannan furuci a yayin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Juma’a, inda ya zargi shugaban kasa da rashin cika alkawarin ingantaccen mulki.

Ya ce babu abin da ya karu sai talautar da al’umma, da kuma tabarbarewar tattalin arzikin kasa.

Ya koka kan manyan sauye-sauyen tattalin arziki, inda ya kaw misalin karancin raguwar tattalin arzikin abun da ake samarwa a cikin ciki (GDP), wanda ya ragu daga Dala biliyan 493 a shekarar 2015 zuwa kimanin Dala biliyan 362 a shekarar 2024.

A cewarsa, wannan raguwar 27% na GDP ya nuna yadda tattalin arzikin Najeriya ke kara tabarbarewa tsawon shekaru tara da suka gabata, abin da ya jefa miliyoyin mutane cikin talauci da koma baya.

Falalu ya kuma soki yadda ake gudanar da kudaden shiga daga cire tallafin man fetur, tsarin canjin kudade da karin farashin wutar lantarki, yana mai cewa ba su samar da kayan more rayuwa da aka yi alkawari ba.

Ya kara da cewa harajin 38% da bankuna ke caji yana hana bunkasar kananan da matsakaitan masana’antu (SMEs), wanda shi ne jigon ci gaban tattalin arziki.

Falalu ya bayyana shirin tattaunawa tsakanin PRP da ADC kan yiwuwar kafa kawance ko hadewa, yana mai jaddada bukatar samun zabe na gaskiya don samun kyakkyawar makoma ga matasa.

Ya fadi fatansa na cewa sauran jam’iyyu su hada hannu wajen hadewa waje guda kafin zabe mai zuwa.

Jam’iyyar PRP ya zargi Tinubu da rusa tattalin arziki

Bafarawa ya ƙaddamar da gwagwarmayar ceto Arewa

Kirsimeti: Zulum ya umarci biyan albashin Disamba kan lokaci