Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya amince da biyan albashin watan Disamba ga dukkan ma’aikatan gwamnatin jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Dauda Illiya, ya fitar a ranar Asabar, an bayyana cewa gwamnan ya amince da biyan albashin ne a ranar Juma’a, 13 ga Disamba, 2024.
Sanarwar ta ce, “Gwamna Zulum ya umarci cewa babu Kirista, Musulmi ko wani dan jihar da zai ji kansa ba tare da jin dadin kasancewa daya daga cikin al’ummar Jihar Borno masu zaman lafiya ba, musamman a irin wannan lokaci na bukukuwan kirsimeti da kuma bayan su, la’akari da hadin kai da zaman tare na al’umma daban-daban a jihar.”
Umarnin Gwamna na fara biyan albashi tun farkon watan Disamba ya yi daidai da jajircewarsa wajen karfafa haɗin kai da ba wa duk mazauna damar shirye-shiryen bikin Kirsimeti ba tare da matsalolin kudi ba.
Sanarwar ta bayyana cewa manufar hakan ita ce taimaka wa Kiristoci da sauran mabiya addinai wajen samun damar shirya bukukuwan Kirsimeti cikin lokaci.
Kirsimeti: Zulum ya umarci biyan albashin Disamba kan lokaci