in

Shugaba Tinubu ya taya iya murnar cika shekaru 90

Shugaba Bola Tinubu ya tura sakon taya murna ga dattijon kasa kuma Farfesa a fannin lissafi, Farfesa Iya Abubakar, dake bikin cika shekara 90 a duniya.

Farfesan ya taba zama shugaban jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya, ya kuma kasance ministan tsaro a jumhuriyar Ta Biyu.

Farfesa Abubakar ya kuma taba zama Sanata mai wakiltar Arewacin Adamawa daga 1999 zuwa 2007.

Tinubu, ta bakin mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya yaba da gudunmawar da Farfesan ya bayar ga kasar nan tsawon lokaci, musamman ta fannin ilmin lissafi da kuma fasahar sadarwa.

Shugaban kasar ya yi addu’ar Allah ya ba wa tsohon Sanatan lafiyar jiki mai kyau domin ci gaba da ba da gudummawa mai amfani ga kasa.

Shugaba Tinubu ya taya iya murnar cika shekaru 90

ASUP ta janye yajin aiki

Kano Pillars na fatan nasara a wasanta da Shooting Stars