SHARE

Toby Okechukwu, tsohon Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai kuma tsohon Shugaban Ma’aikata na Mataimakin Kakakin Majalisa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP.

A wata wasikar murabus da aka sanya wa hannu ranar 6 ga Disamba, 2024, kuma aka aika wa shugaban PDP na mazabarsa ta Owelli/Amoli/Ugbo/Ogugu a Karamar Hukumar Awgu, Jihar Enugu, Okechukwu ya gode wa jam’iyyar bisa ba shi dama don hidimtawa al’ummarsa.

Okechukwu, wanda ya wakilci mazabar Aninri/Awgu/Oji River a Majalisar Wakilai ta kasa a zabubbukan 7, 8, da 9, yayi bitar shekarun hidimarsa a cikin wasikar.

“Na rubuto muku don sanar da murabus dina daga jam’iyyar PDP tare da nuna godiyata matuka ga jam’iyyar bisa damar da ta bani na wakiltar al’ummar mazabar tarayya ta Aninri/Awgu/Oji River a zabubbuka na 7, 8, da 9 na Majalisar Wakilai,” wani bangare na wasikar ya bayyana.

Murabus dinsa ya biyo bayan nadin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi masa a matsayin Daraktan Ayyuka na Hukumar Ci Gaban Yankin Kudu Maso Gabas.

Tsohon mataimakin marasa rinjaye, Toby Okechukwu yabar PDP

NO COMMENTS