Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta ce masu garkuwa da mutane sun karɓi kusan Naira tiriliyan 2.2 a matsayin kudin fansa cikin shekara guda.
Rahoton hukumar ya kunshi inciken, wanda ya sassan Najeriya a birane da karkara da matsalar garkuwa da mutane ta fi ƙamari a tsakanin watan Mayu 2023 zuwa Afrilu 2024.
Rahoton ya kuma bayyana cewa garkuwa da mutane ya fi yawa a yankunan karkara fiye da birane.
Rahoton, wanda aka wallafa ranar Talata, ya yi nazari kan laifuka daban-daban da ake aikatawa a fadin kasar da kuma wuraren da ake yawan samun irin wadannan laifuka.
Rahoton ya kara da cewa fiye da rabin iyalan da suka fuskanci garkuwa sun biya kudin fansa domin samun ‘yancin ‘yan uwansu.
An kuma bayyana cewa matsakaicin kudin da aka biya a matsayin fansa ya kai Naira miliyan 2.7 a kowanne lokaci.
Yankin Arewa maso Yamma ya fi sauran yankuna yawan kudin fansa da aka biya, inda ya kai Naira tiriliyan 1.2, yayin da Kudu maso Gabas ta fi kankanta da Naira biliyan 85.4.
Binciken ya nuna cewa Najeriya ta samu rahoton garkuwa da mutane guda 2,235,954.
Yankunan karkara sun fi yawan irin wannan laifi da alkaluma 1,668,104, yayin da birane suka samu 567,850.
Jihohin da ke Arewa maso Yamma sun fi yawan rahoton garkuwa da mutane, yayin da Kudu maso Gabas aka samu karancin masu yin hakan.
“An kiyasta yawan garkuwa da mutane a matakin kasa zuwa 2,235,954. Sakamakon ya nuna cewa yankunan karkara (1,668,104) sun fi yawan garkuwa fiye da birane (567,850). Karin bincike a matakin yankuna ya nuna cewa Arewa maso Yamma ce ta fi yawan rahotannin garkuwa da mutane da 1,420,307, sai Arewa ta Tsakiya (317,837), yayin da Kudu maso Gabas ce ta fi kankanta da 110,432,” in ji rahoton.
An kashe ₦2.2tr wajen biyan kudin fansa a 2024, Arewa maso Gabas ce a gaba